1. Hawan Jini; Wannan jinya ce dake haifar da illoli ga lafiyar mutum daga ciki har da raunata da namiji.
2. Ciwon Siga; Hakanan shi ma wannan ciwo idan ba ai da gaske ba yana iya kashe mazakuta gaba daya.
3. Ciwon Sanyi; Ciwo ne da ake dauka yayin jima’i ko bayan gida maras tsafta, kuma yana shafar al’aura ne, saboda haka ya na iya raunata mutum kwarai da gaske.
4. Basir; Hakazalika wannan ciwo ba karamar illa ya ke yi wa maza ma’aurata ba.
5. Matsananciyar Damuwa; Matukar mutum na cikin irin wannan yanayi, akwai matukar wahala sha’awarsa ta motsa ballantana ya samu mikewar azzakari.
6. Shan Taba; Ta na haifar da matsalolin lafiya ga dan-adam daga ciki har da illata hanyoyin jini da sauran gabobi da ke da matukar tasiri wajen mikewar gaban mutum.
7. Shan Giya; Khamru uwar laifi, ta na kan gaba wajen illata lafiyar dan adam gami da kashe ma sa azzakari.
8. Rashin Isasshen Abinci Mai Gina Jiki; Abincin da mu ke ci na da kyakkyawar alaka da lafiyarmu, saboda haka rashin sa na nakasa lafiyar jikinmu har da sha’awa da karfin mazakuta.
9. Rashin Motsa Jiki; Ba shakka rashin motsa jiki kan iya illata mutum ta fuskar gamsar da iyali, wannan ya hada da rashin karfi da saurin kawowa.
10. Wasu Magunguna; Abin nufi anan shine wasu magungunan cutar da mutum ke sha ka iya haifar da raunin mazakuta, misali daga cikin magungunan da ake bai wa ma su hawan jini akwai ma su wannan illar.
11. Hadari; Idan hadari ya rutsa da mutum kuma ya shafi al’aura ko hanyoyin jima’i, kamar ‘ya’yan maraina, azzakari, ko jijiyoyin da su ke da alaka da jima’i hakan kan haddasa rauni ga namiji.
13. Wasu Nau’ikan Abinci; Akwai wasu nau’ikan abinci da ke ragewa namiji sha’awa da kuzari yayin jima’i.
14. Shan Miyagun Kwayoyi; Shan miyagun kwayoyi ko kuma shan kwayoyin barkatai ba bisa ka’ida ba kamar yadda mu ka ambata a sama, ko da kuwa kwayoyin na magani ne.
15. Rashin Isasshen Barci; Ya na da matukar tasiri wajen ragewa namiji kuzari yayin saduwar aure, ya na da kyuu mtum ya samu isasshen barci a kullum, akalla awoyi 7-8.
16. Kallon Fina-finan Batsa; Masana sun gudanar da bincike na zamani kuma sun gano tare da tabbatar da gagarumar illar da hakan ke haifarwa maza musamman ta bangaren jima’i.