Namijin goro tana daga cikin itatuwa masu amfani ga lafiyar dan Adam, ta hanyoyi da dama akan abinda ya shafi garkuwar jiki har zuwa ga Karfin mazakuta.
Bisa wannan dalili yasa muka ga ya dace muyi amfani da damar da muke da ita, mu sanar daku yanda zaku magance ciwon sanyi da namijin goro.
Zaki nemi kayan hadi kamar haka:
~ Namijin goro
~ Citta mai yatsu
~ Tafarnuwa
~ Zuma mai kyau
~ Lemun tsami
Bayanin Yadda Za’a Hada
Zaki Samu citta da namijin da tafarnuwa ki jajjaga ki kuma yanka lemun tsami ki tafasa da bawon tare da sauran kayayyakin, idan ya dafu sai ki tace ki dunga sha kaman shayi rabin kofi sau uku a rana na sati 2.