Wata yarinya da iyayenta suka yi ta nemanta tsawon kwanaki uku bayan ta fita wasa tare da abokananta, anyi nasara ganota a cikin rijiya wacce babu ruwa a cikin ta.

A wata wallafa da muka samu daga shafin “Labarun Hausa” wata yarinya wacce ‘yar shekaru uku ce a duniya ta bata tsawon kwana uku bayan da ta fita wasa da abokananta, har aka nemeta aka hakura.

Shafin na “Labarun Hausa” sun ruwaito labarin kamar haka:

An tsinci wata karamar yarinya “Lydia Azatyom” mai shekara uku a duniya a cikin wata tsohuwar rijiya, kwanaki uku bayan tayi batan dabo a unguwar Tudun Wada ta Jos, babban birnin jihar Filato.

Ganin karshe da aka yiwa karamar yarinya ya auku ne a ranar Alhamis 27 ga watan Oktoba, tana wasa da kawayenta a kofar gidan su kafin bacewar ta.

Duk wani kokarin iyayenta da makwabta na ganin an gano inda take yaci tura, har sai zuwa bayan kwana uku, lokacin da wani Dauda Dung ya tabbatar da cewa an gano ta.

Shafin LIB ya ambato cewa, wani matashi ne ya gano yarinyar a cikin wata tsohuwar rijiya a wani kango dake unguwar.

An tattaro cewa, matashin yaje kangonne domin yin bayan gida inda yaji karar alamun motsi a cikin rjiyar wacce bata da ruwa.

Ginin kangon dai an dade ba’a amfani da shi inda yanzu aka mayar da shi wurin zubar da shara da yin bahaya.

Lydia ta samu raunika a wajen kanta inda aka garzaya da ita asibiti inda take cigaba da samun kulawar da ta dace.

Har yanzu dai ba’a da masaniyar cewa ko yarinyar bisa tsautsayi ta fada cikin rijiyar ba ko kuma wani ne ya jefata ciki.

Source of “Labarun Hausa

By Mismob

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *