A wani labari da muka samu daga shafin “Labarun Hausa” wanda ya dauki hankulan mutane da dama, inda wani bakar fata dan Nageriya ya yi wuff da wata zankadediyar Baturiya.
Mutumin wanda ya shahara a dandalin TikTok wanda yake da dubbannin al’umma, ya wallafa bidiyon sa tare da Baturiyar inda har aka ganota tana yi masa shidimar girki wato tana dafa masa abinci.
Bidiyon ta dauki hankulan jama’a da dama duba da yadda aka ga Baturiyar ta saki jiki tana abubuwa irin na ‘yan Nageriya ba tare da damuwa ba.
Shafin “Labarun Hausa” sun wallafa cikekken rahoton inda a kasa kuma zakuga bidiyon mutumin tare da Baturiyar tasa, ga cikekken rahoton a kasa.
Wani matashi dan Najeriya mai amfani da suna @kanorsamuel223 a manjajar TikTok, ya saka wani bidiyon budurwar sa Baturiya a kafar.
Wani bangare daga cikin bidiyon ya nuna kyakkyawar baturiyar na amfani da tukunyar gas tana soya masa filanten, ta nuna cewa lallai ita fa taga wurin zama.
ldan da ba domin yana yin kalar fatar jikinta ba, da sai ayi tunanin cewa ‘yar Najeriya ce bisa yadda ta gudanar da dafa abincin.
Mutane da dama sun yi tururuwar zuwa bangaren yin sharhi domin tambayar matashin yadda akayi ya samu wannan kyakkyawar baturiyar a matsayin budurwar sa.
Akwai akalla sama da mutum 400 da suka yi sharhi a kan bidiyon, yayin da sama da mutum dubu sha bakwai suka danna alamar so akan bidiyon.
Ga kadan daga cikin mutanen da suka tofa albarkacin bakin nasu akan bidiyon.
Alex George ya rubuta: Pablo kayi kokari, lokacin ka ne na tunawa cewa lallai akwai so na gaskiya, ‘yan uwanta kar mu yasa nace maka nagode.
halo ya rubuta: Dan’uwa ya samu nasara a rayuwa, yoooooo.
Dandy McCarthy ya ributa: Surkullenka mai karfi ne.
TikToker ya rubuta: Ya samu katin zama dan kasa.
washy ya rubuta: Har yanzu ina ta tunanin abinda za’a samar.
Source of “Labarun Hausa”
Ga bidiyon a kasa domin ku kalla.