Fitaccen mawakin siyasar nan a Najeriya Dauda Kahutu Rarara ya bayyanawa duniya wasu abubuwa dangane da takaddamar sa da Gwamnan jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje.
Mawakin yace, ko gidan sa akan layin lantarki yayi yasan Ganduje ba zai rushe masa ba sai dai idan wani zai gina masa.
Domin gidan sa Gwamnati ce ta gina sa shi kawai abunda yayi shine kara sabunta shi.
Haka kuma ya kara da cewa, a shekarun baya lokacin zabe sak da akayi ita ta haifar da sakarkaru da ake ta fama dasu yanzu haka.
Haka kuma ya bayyana wasu mawaka da suke neman inda gineginen sa da kadarorin sa suke domin su sa’a talauta shi.
Sai dai mawakin bai bayyana sunan mawakan biyu daya fada a fakaice ba, ba tare da bata lokaci ba zaku iya kallon cikakken bidiyon anan kasa.
Ga cikekkiyar bidiyon a kasa domin ku kalla.