Yawanci idan mura ta kama mutum yana iya warkewa a cikin kwanaki hudu zuwa bakwai zaka iya rage jin ciwon domin ka warke da wuri. Akwai hanyoyin da zaka iya amfani dasu tare da magungun da kuma wadanda ba’a amfani da magunguna.

Hanya ta daya: Bude hanyar iskar ta hanci

1. Shan abu mai dumi sosai. Idan kana yawaita shan abubuwan da suke da dumi zasu sa majinar dake cikin hancin naka ta narke. Binciken masana ya nuna cewa shan abu mai dumi yana rage ciwon mura, sanyi, makogwaro, tari da kuma gajiya. Idan kana da shayi zaka iya sha amma kar ka saka nescafe a ciki. Amma kuma a guji shan giya domin tana jawo kumburi da toshewar kofar hanci.

2. Yin wanka da ruwan dumi. Ka sami ruwan dumi kayi wnka dashi ko kuma ka shiga cikin ruwan ka zauna. Zaka iya tafasa ruwa ma a tukunya idan ya fara tafasa sai ka sauke ka zuba a cikin roba ko wani abu mara daukar zafi sosai. Sai ka dinga matsar da kanka zuwa saman robar ko kuma kayi amfani ko tawul wajen lullube kan naka har sai ka shaki tiririn kamar na mintuna goma. Zaka iya yin wannan sau daya zuwa biyu a rana.

3. Kayi abinda bature yake kira da “Oil pulling”. shi wannan abunda ake kira da oil pulling tsohuwar hanya ce da mutane suke amfani da mai wajen cire kananan kwayoyin cuta daga baki. Domin kuwa yawanci wadannan kwayoyin cutar suna makalewa a jikin mai da kuma kitse, wanda hakan zai baka damar furzar dasu tare da mai daga bakinka.

– zaka iya amfani da man kwakwa domin kuwa yana dauke da sinadarin da yake kashe kwayoyin cuta. Idan kuma baka samu ba zaka iya amfani da man ridi (kantu).

– kar ka hadiye man bayan ka kuskura a bakinka, idan kaga alamar zaka iya hadiyewa sai ka furzar da kadan daga bakin naka.

– bayan ka gama kuskurewa sai ka zubar/furzar da man, daga nan kuma sai ka kuskure bakinka da ruwan dumi.

4. Ka bushe hancinka dai-dai. Yana da muhimmanci ka dinga bushe hancinka idan mura ta kama ka, amma kuma kar ka dinga bushe shi da karfin gaske. Domin kuwa idan kayi da karfi zai iya shfar kunnen ka wanda zai iya jawo maka ciwon kunna bayan kuma mura da take damunka. Ka tabbatar da cewa ka bushe hancin naka a hankali sannan kuma ba ko da yaushe ba sai ta kama.

– likitoci suna bada shawarar cewa idan zaka baush hancinka ka kayi amfani da dan yatsa daya wajen toshe kofar hanci guda sannan ka bushe dayan.

– yana da kyau ka dinga wanke hannunka bayan ka bushe hanci domin ka wanke kwayoyin cuta da zasu makale bayan bausar da kayi.

Hanya ta biyu: amfani da albarkatun halitta

1. Shan “elderberry”. shi wannan abun ana amfani dashi sosai ajen yin magunguna. Yana iya kashe kwayoyin cuta kuma ya rage kumburi daga jiki. Yana zuwa a magani na kwaya ko na ruwa, a wasu lokutan ma ana samunsa a alawar da za’a tsotsa. Idan kuma kuna da ganyen a gida sai a daka shi a dinga hada shayi dashi. Amma kuma a lura kar ayi amfani dashi na lokaci mai tsayi ba tare da an tuntubi likita ba musamman ga mata masu ciki, hawan jini ko ciwon suga. Ana samunsa a shunan siyar da magunguna.

2. Ayi amfani da ‘Eucalyptus’. Eucalyptus yana zuwa a matsayin kwayoyi, magani na tuwa ko kuma maganin zubawa a ruwan zafi. Yawancin magungunan mura na dauke da sinadirin eucalyptus. Akwai kuma eucalyptus da ake siyarwa wand shafawa ake, saboda haka sai a shafa a kan hancin. Bayan an siyi maganin sai a tambayi kuma yadda ake amfani dashi a wajen.

3. Amfani da ‘peppermint’. shima wannan ganye ne amma ana iya samunsa a shagunan siyar da magani. Yana zuwa a matsayin alawar da ake tsotsa. Abinda yake da amfani a cikinsa wanda yake maganin mura ana kiransa ma menthol. Saboda haka idan aka je nemansa za’a iya cewa maganin mura mai dauke da menthol ake nema. Akwai wuraren da suke siyar da ganyen shayin peppermint wanda zaka iya hada shayi dashi. Yana iya zuwa a matsayin man shafawa kamar missaleta ko robb.

4. Amfani da danyar zuma. Zuma tana magani daban-daban a jikin mutum. Tana karawa sojojin jikin mutum karfi domin su yaki cuta sannan ita da kanta ma tana yakar kwayoyin cuta. Domin ka samu amfani sosai ka nemi zumar da aka samo da wajen samowa ba tare da an sarrafa ta a kamfani ba. Ba’a bada shawarar a dinga bawa jaririn dake kasa da shekara daya zuma. Sannan kuma za’a iya zuba zumar a shayi ko a hada ta da lemon zaki domin maganin mura.

5. Amfani da tafarnuwa. Tafarnuwa tana taimakawa jikin mutum sosai wajen yakar cututtuka. Bincike yana nan akan yadda tafarnuwa take warkar da mura. Zaka iya cin tafarnuwa a cikin abinci ko kuma ka sha kwayoyin ta da ka siya daga shagon magani.

Hanya ta uku. Taimakawa jikinka ya warke da wuri.

1. Kuskura ruwan gishiri. Idan ka sami ruwan dumi kamar kofi daya sai ka zuba gishiri cokalin shayi sannan ka dinga kuskurawa a baki bayan minti daya ka zubar, ka kara zuba wani a baki bayan minti daya ka zubar. Kayi hakan kamar sau uku ko hudu a rana. Amma kar a dinga sawa yara suna kuskurawa dominzasu iya shanye ruwan gishin.

2. A sha Vitamin C. vitamin C baya warkar da ciwon mura ko sanyi, amma kuma yana taimakawa jikin mutum wajen yakar ciwon. Kwayoyin vitamin C suna zuwa a matsayin 50mg ko 100mg saboda haka kar a sha sama da 2000mg a rana daya. Lemon zaki ma yana dauke da sinadarin vitamin C haka zalika ja da koren tattasai da sauran kayan lambu. Kar a dinga shna vitamin C sama da ka’ida domin kuwa zai biyo fitsari ne ya fita.

3. A sha ruwa sosai. Idan ana fama da mura ko ciwon makogwaro yana da kyau ka zamana ko yaushe akwai ruwa a cikin jikinka. Kar ka zamana kana jin kishirwa kafin ka sha ruwan. Mata ana bukatar su n=dinga shan ruwa kamar kofi tara kullum, maza kuma kamar kofi goma sha uku idan ana da lafiya ma kenan. Idan kuma ana rashim lafiya sai a shirya shan sama da haka ma. A guji shan giya da kuma abubuwan dake dauke da kofee.

4. Ka sami hutu sosai. Jikinka yana bukatar hutu domin ka warke da wuri. Idan ka fiya wahalar da kanka zai sa sojojin jikinka su kasa yakar cutar.
– ka dinga kokarin yin baccin rana sosai sannan kuma idan kana samun matsalar numfashi idan kana bacci sai ka daga kanka da pillow.

Hanya ta hudu. Neman taimakon masana.
1. A nemi likita idan numfashi yana daukewa ko fito a cikin numfashin. Duk lokacin da ka sami matsalar shakar numfashi to wannan ya kamata ka nemi likita.

2. A nemi likita idan zafin jiki ya wuce 38.5oC ko kuma ya wuce kwanaki biyar. Idan mura ce kawai zazzabin zai tafi da wuri. Amma idan taki tafiya hakan yana nufin al’amarin ya karfafa kenan. Likita zai gano dalilin hakan sannan ya bada magani. Idan kuma yaro ne to idan zazzabin ya wuce kwanaki biyu sai aje ganin likita.

3. Ka nemi taimako idan alamu sukayi tsanani ko kuma suka ki yin sauki a kawanaki bakwai. Kamar yadda na fada, yana warkewa a cikin kwanaki bakwai idan kaga baka sami sauki ba to ciwon yayi karfi kenan ko kuma kana dauke da wata cutar ne. Zaka iya samun wadannan abubuwan:

– Zazzabi
– Ciwon makogwaro mai tsanani
– tari mai tsanani
– ciwon karan hanci
– yoyon hanci
– ciwon jiki
– atishawa

4. Ayi gawji domin tabbatarwa ba wata cutar bace. Mura tana iya yin kamanceceniya da wasu cututtuka hanyar nunfashi, saboda haka likita zai iya sawa ayi maka gwaje-gwaje domin gano asalin matsalar.

A takaice
A lura da wadannan abubuwan:
– Shan abu mai dumi sosai.
– Yin wanka da ruwan dumi.
– Kayi abinda bature yake kira da “Oil pulling”.
– Ka bushe hancinka dai-dai.
– Shan “elderberry”.
– Ayi amfani da ‘Eucalyptus’.
– Amfani da ‘peppermint’.
– Amfani da danyar zuma.
– Amfani da tafarnuwa.
– Kuskura ruwan gishiri.
– A sha Vitamin C.
– A sha ruwa sosai.
– Ka sami hutu sosai.
– A nemi likita idan numfashi yana daukewa ko fito a cikin numfashin.
– A nemi likita idan zafin jiki ya wuce 38.5oC ko kuma ya wuce kwanaki biyar.
– Ka nemi taimako idan alamu sukayi tsanani ko kuma suka ki yin sauki a kawanaki bakwai.
– Ayi gwaji domin tabbatarwa ba wata cutar bace.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *