.

Wasu matan daga sun yi haihuwa daya sai aga nononsu ya zube, hakan yana damun maigida sosai, idan kina san yin maganin wannan matsala akwai abubuwan da suka kamata ki nema kamar haka :

● Habbatussauda
● Hulba
● Alkama
● Gyada
● Ridi
● Danyar shinkafa
● Busasshe karas.

Duk ki daka su waje daya, kina yin amfani dashi a duk wani sa’i wane lokacin kina amfani da wannan hadi.

・ YADDA ZA’A GYARAN NONO

Tabbas matsalar nono tana da yawa domin zaka ga wasu matan nonon su ya kwanta ko ya koma dan kankanin saka makon tso-tso idan kina San ya taso Yayi kyau sai kiyi wannan hadin ki gani.

– Albasa madaidaiciya
– Zuma
– Garin gero
– Madara.

Ki samu albasa madaidaiciya ki yanyanka sai ki saka a tukunya da ruwanki ta tafasa shi sosai har sai ruwan ya koma baki, sai ki juye ruwan ki sami zumar ki mai kyau, garin gero ludayi daya, madara na gwangwani daya na ruwa sai ki juye su kan ruwan tafasasshe albasa nan ki sha.

Amma fa karki bari ya kwana baki shanye ba.

Wannan hadine da zai gyara miki nono.

WATA HANYAR TA DABAN DON GYARAN NONO

Idan Ana so nono yayi kyau yayi laushi da sulbi da girma sai Ayi wannan hadin domin samun waraka.

– Aya
– Gyada
– Ayaba (plantain)
– Alkama
– Madara

Ki sami aya, gyada ayaba da alkama sai madara Zaki wanke ayarki sai ki hada da gyadarki ki markada su ki tashe dama kin yanyanka ayabarki kin busar kinyi gari da shi kin tankade sai ki rikka diban garin plantain din kina hadawa da ruwan ayaba gyadarki kina sa madara ta ruwa kina sha, zai gyara nono domin wannan hadin ne Wanda sai kisha mamaki.

HADIN CIWON SANYI

– Hulba
– Bagaruwa
– Man habbatussauda

Yadda za’a yi shine.

A hada bagaruwa da hulba a tafasa sai idan ya dan huce sai a zauna ciki sannan kuma ashafa man habbatussauda kamar yadda za’ayi matsi Wadannan magunguna da akayi amfani dashi zai magance MATSALAR ciwon sanyi sannan kowane yana Kara dawwamar da ni’ima ga mace.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *