A lokuta da dama mata suna fama da ciwon nono mai tsanani, wanda hakan yake zama babbar barazana ga rayuwar su baki daya. Akwai hanyoyi da dama da mace zata bi domin ganin ta magance matsalar da take damunta a mamanta (nononta).
Sau da yawa ciwon nonon yana faruwa ne bisa wani dalili da yake bayyananne ko kuma boyeyye ga mace, inda za’a ga nonon ya kumbura, ko yana fitar da ruwa mai wari sabanin ruwan nonon. Domin magance wannan matsalar, sai kiyi wannan hadi.
Zaki nemi kayan hadi kamar haka :
– Garin shammar
– Garin hulba
– Ganyen jirjir
– Zuma
Bayanin Yadda Zaki Hada :
Zaki samu dukkan kayan hadin sai ki tafasa ki zuba zuma sai ki dunga sha har zuwa lokacin da zai kare. InshaAllah za’a samu biyan bukata.