A lokuta da dama zaku ga macen da tayi haihuwa daya zuwa uku, gaba daya ta rikece tamkar wanda ta shayar da garken shanu da nononta, ma’ana duk sun zube sun koma kasa tamkar masu ciren ciyawa a gona.
Wannan ba kamata bane, musamman dangane da mace wadda ainashi dama an santa da kwalliya da kuma gyara jiki. Don haka dole sai uwargida ta zage damtse wajen tabbatar da ganin ta gyara jikinta, ko don yara na kasa da ita.
Bisa wannan dalili shafin “Mismob” suka ga ya dace suyi muku karin haske tare da fayyace muku hanyar da zaku bi domin gyara kayan ku.
Saboda haka abinda zaki nema sune kamar haka ;
– Garin bulba
– Garin waken soya
– Garin gyada wanda aka soyata sama sama.
Bayani Game da Yadda Za’a Hada
Bayan kin samu wadannan kayan hadin, sai ki hadesu guri guda ki gauraya, ki dunga diba kina sha da madara peak har zuwa lokacin da zai kare, da yardar Allah zaki ga abin mamaki ga nononki.