• Ridi:

Maza masu fama da raunin mazakuta suna iya amfani da Ridi, su yawaita cinsa, yana amfani sosai wajen magance raunin na su.

• Albasa:

A yayin wasu sinadaran ke amfani wajen dadewa a yayin jima’i, masana sun tabbatar cewa albasa tana daya daga cikin nau’o’in sinadaran da ake amfani da su wajen karin yawan ruwan maniyyi a jikin dan adam.Haka kuma masanan sun tabbatar cewa Albasa tana taka muhimmiyar rawa wajen karin girman al’aura musamman ga maza.

DOMIN KARIN NI”IMA

• Alkama:

Garin alkama na daga cikin nau’o’in abincin da ma’aurata ke bukata wajen karin ni’imar aure.

Yadda ake sarrafa shi kuwa shi ne, ana samun garin alkama a hada shi da nono mai kyau, ko madarar shanu, wadda aka tatsa yanzu-yanzu, a rinka hadawa da ruwan dumi ana sha.

Hakan yana magani sosai wajen mu’amala tsakanin mata da miji, musamman kara dadewa a yayin jima’i.

・ DOMIN ƘARFIN GABA

• Ayaba:

Ana kwadaitar da ma’aurata su yawaita cin ayaba, masana sun tabbatar cewa ita ma Ayaba tana karawa namiji karfi matukar gaske*

・DOMIN RAUNIN GABA

• Jirjir:

Yana matukar amfanin musamman ga maza, idan aka hada shi da Habbarashid, yana kara karfi sosai musamman ma ga wanda yake da rauni sosai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *