Yan uwa ina yiwa kowa fatan Alkhairi,a yau insha Allah zan baku wani babban sirrin ga masu fama da matsala ta karancin maniyy.

Ko wanda maniy nasa matattun sunfi masu rai yawa,ko wadan da maniy nasu baya fita yadda ya kamata to ga wannan fa’ida agi kokari a jarraba ta insha Allah zaa dace.

ABINDA ZAA NEMA:

Za’a samu yayan kabewa,amma kabewar wacce ta nuna sosai sai gyara su a shanya su bushe a inuwa bayan nan zaa dake su sosai su zama gari.

Za’a rika diban karamin chokali (teaspoon)ana zuwbawa a madara da ruwa peak milk rabin gwangwani a sha safe da yamma.

Idan peak tana bata maka ciki sai ka samu nono mai kyau mara tsami ka hada dashi kana sha,sannan zaa sha wannan tsawon sati 3 zuwa wata guda.

Amma idan mutum Allah bai bashi haihuwa ba sandiyyar karanci ko tsinkewar maniyy,sai ya rika hakurin rage jima’i,ya rika yi kamar sau 2 ko 1 a sati,domin wannan shine zai bawa maniy damar zama cikakke wanda zai iya samar da ‘da.

Allah yasa mu dace .

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *