YANAR MAHAIFA ( FIBRO ) matar da take fama da cutar mahaifa wato fibro zata iya samun garin hulba da garin khustul hindi, da garin habba, ta sanya su cikin madara ko nono tana sha sau uku a wuni insha Allah.

KAIKAYIN GABA ( INFECTION ) matan da take fama da cutar infectoin na mahaifa, tana iya samun waken suya, aya, albasa,tafarnuwa,hulba,khutul hindi, ta tafassa su taba sha, sau uku a wuni insha Allah kuma zata dinga tafasa su taba sha, sau uku a wuni,

ko ta dinga tafasa hulba da tafarnuwa da albasa tana shiga ciki.

ko ta samu albasa, tafarnuwa, hulba, ta tafasa su, ya zama ruwan shan ta, bisa matsala na kurajen mahaifa amma banda mai ciki na sha.

CIWON MARA LOKACIN AL’ADA DA KUMA ZAFIN FITAR FITSARI GA NAMIJI KO MACE.

asami harmal a dakashi a hada da khaltit da yansun sai a rinka dafawa kamar shayi ana sha da zuma kullum cokali 1+1+1 sau uku a rana kenan.

CIWON ZUCIYA: idan mutum yana fama da ciwon zuciya ya samu karamin cokali na garin habbatussauda a hadashi da zuma a zuba a cikin ruwan zafi ko shayi sai a sha kullum safe da yamma.

KUMBURIN HANTA: idan mutum yana fama da kumburin hanta, za’a samu garin habba karamin cokali a hadashi da garin kurna babba cokali biyu sai a hadasu kullum sau uku amma ya zama maganin cokali uku uku sau uku a wuni.

TYPOID asamu garin hulba da ganyen magarya da garin habba da tsamiya sala daya da zuma cokali uku a rika tafasawa ana sha.

ULSER ana amfani da garin hulba da garin habba da zuma a gauraya su waje daya a dinga sha safe kafin a karya, sai bayan awa daya aci abinci haka da rana haka da dare.

ko a sami hulba a dinga sha da zuma za’a samu lafiya.

MATSALOLIN MAZA

RAUNIN AL’AURA:
Namiji da yake fama da raunin al’aura ba’a cewa ya sha magani kaza, sai anyi masa bincike guda uku,

1. A duba a gani baya da ciwon sugar?
saboda cutar sugar tana sabbabar da raunin al’aura.
in yana da ciwon sugar a kwai maganin da zaiyi amfani da shi.

2. Sannan sai a duba yana da basir?
In yana da shi akwai hanyoyin da ake bi a magance shi.

3. A duba a gani baya da gajiya da talauci, ko yawan aiki ko damuwa, domin shima yana kawo raunin al’aura saboda hankalinsa bai natsu ba balle yayi sha’awa.

KA DAURE KAYI WADANNAN MAGANIN MAIGIDA

Ciwon sugar :

Man hulba da zaitu ( jonifer oil ), habba yar’algeriya, zaitu lauz, sai a hada su waje daya kafin ka kwanta da dare da awa daya, za’a samu madara musamman na luna, sai a dumama su tare da zuma a gauraya shi ana sha da safe kafin a karya, za’a dace Insha Allah.

Idan kuma babu ciwon sugar yana son ya samu kusancin matansa, sai ya samo hulba tare da matan zasu sha tare kafin su kwanta da awa daya, wannan yana taimakawa sosai.

Damuwa sai a rage ta sosai da shan sugari duk.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *