A safiyar yau ne muka tashi da wani labarin abin farin ciki da ya sami tsohuwar jarumar masana’antar kannywood “Ummi Rahab”, wacce a yanzu take Mata ga Mawaki Lilin Baba.

Tsohuwar jarumar ta wallafa wata sanarwa ne a shafin ta na sada zumunta Instagram, inda take bayyana cewa a yanzu haka tana dauke da juna biyu.

Shafin “Fim Magazine” dake kan dandalin sada zumunta na Instagram suka sun kawo cikekken rahoton kamar haka.

Matar mawaki furodusa kuma jarumi Shu’aibu Ahmed Abbas Lilin Baba kuma tsohuwar jarumar Kannywood Rahama Saleh Ahmed Ummi Rahab, ta bayyana cewa ta samu ciki.

Ummi ta ba da wannan sanarwar ne a Instagram inda ta wallafa hoton ta sanye da jar atamfa, ta na zaune a kan kujera ta na murmushi.

A sakon ta rubuta da Turanci da manyan bakake inda take cewa:

Im pregnant, wanda mujallar Fim ta fassara da, Na samu ciki, Jarumar mai ritaya ta yi kira ga masoyan ta dasu taya ta murna.

Har ta yi alkarin za ta ba da tukwicin katin waya ga mutum 50 na farko da suka tura sakon murnar a kasan hoton nata.

Ta ce: Idan na samu ‘comments’ ta hanyar rubuta ‘Congratulations’ a karkashin wannan hoton, zan ba da kyautar kati ga mutane 50.

Sai dai ba ta fadi ko katin nawa din za ta ba kowane mutum ba, haka kuma matar ta Lilin Baba ba ta bayyana ko cikin nata dan wata nawa ne ba.

Dimbin masu bibiyar ta a Instagram sun taya ta murna tare da taya ta fatan alheri.

Ita dai Ummi, an daura auren ta ne da Lilin Baba a ranar Asabar 18 ga Yuni 2022, a Tudun Murtala Kano, a kan sadaki N200,000 wanda jarumi Ali Nuhu shi ne waliyyin ango shi ne ya karbi auren.

Source of “Fim Magazine

By Mismob

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *