Kamar yadda kuka sani Rahama Sadau ficacciyar jaruma ce a masana’antar kannywood da Nollywood, wanda ta sami lambobin yabo da dama akan harkar tasu ta fim.

A wani labari da muka samu a yanzu daga shafin “Hausaloaded” sun wallafa rahoton yadda jaruma Rahama Sadau tayi nasarar cin kyautar gwarzuwar jarumar kasashen Afirika.

Shafin na “Hausaloaded” suna wallafa rahoton kamar haka: Jarumar fina-finan kannywood “Rahama Sadau” ta zama gwarzuwar jarumar fina-finan ta kasashen Afirika a “Nollywood” a gasar kasa da kasa ta Toronto Amurka.

Wannan labarin dau shine yake ta yawo a kafafen sada zumunta inda shafin labaran kannywood dake manhajar twitter suka wallafa cewa, da fim din Almajiri wanda shine ya baiwa wannan jarumar nasarar lashe wannan kyautar.

Super Star  @Rahma_sadau Tayi Nasarar cinye Gasar Best actress a bikin Toronto International Nollywood Film Festival Canada da film din #Almajiri  Muna Alfahari dake #AFRIFF2022″.

Nan take jaruma Rahama Sadau ta wallafa sakon jin dadi da murnar samun wannan gagarumir nasara da Allah ya bata a shafin na sada zumunta na Instagram inda take cewa:

Na lashe KYAUTA JARUMAR AFRICA tare da ALMAJIRI a bikin Fina-finan Nollywood na Duniya a Toronto.

Lokacin da na sami sunan, na gaya wa kaina cewa ya isa in yi murna da alfahari. Ban san cewa a zahiri jaririn yana zuwa gida gare ni ba. Abinda ban tsamanin ba.

Godiya ta musamman ga maigidana @aycomian don irin wannan dama mai ban mamaki, da yarda da ni.@tokamcbaror don kasancewarsa sihirin da ya kasance koyaushe. Babu ɗayan waɗannan da zai faru ba tare da ƙirƙirar ku ba. Taya murna ga daukacin tawagar. Yanzu, BA ZAN IYA JIRA DUNIYA TA GA ALMAJIRI BA.

Na gode @tinffestival #MarkYourCalendar #3Dec #Almajiri #BestAfricanActress #Tinff.

Ga hotunan da jaruma Rahama Sadau ta wallaha a shafin nata na sada zumunta Instagram.

By Mismob

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *