Hanyoyin magance saurin inzali suna da yawa , wasu hanyoyin na yiwa wasu aiki, wasu kuma sabanin haka , don haka ga hanyoyi kamar haka da mutum zai iya jarrabawa domin neman dacewa:
1 A nemi citta (ginger) musamman ɗanya, a wanke a kuma karkare ta , sa’annan a dake ta , ayi shayi da ita , bayan an tashe ta a kofin shayi sai a zuba zuma ta bada ɗanɗano asha shayin da ɗumi. Ayi hakan safe da rana.
Citta nada sinadari mai zafi na “gingerol” mai sanya yawan gudanar jini ga laura , wanda hakan na sanya ƙarfin gaba da jinkirin kawowa.
2 A nemi man na’a-na’a (peppermint oil) mai kyau, musammman ɗan Misra ko na kamfanin Hemani (Pakistan) . A wanke gaba da ruwan dumi , a goge lemar sa’annan a shafa man ga zakari ya shiga fata, ga kai (glans) da tsawon sandar zakari (shaft) , amma banda kofar fitsari (urethra).
Musamman a shafa idan zakari yana mike, sai jira bayan minti 10 zuwa 15 sa’annan a sadu da iyali. Man na’a-na’a na rage “sensitivity” na zakari , wato rage kaifin ɗanɗano da zakari keji ta yanda zai hana kawowa lokacin jima’i.
Haka kuma za’a iya amfani da man kanimfari (clove oil) mai kyau a maimakon man na’a-na’a. Bugu da kari, man kanimfari na maganin karfin gaba.
3 Fita daga gaban mace na ‘yan mintoci a lokacinda mutum yaji ya kusa kawowa, da kuma fita daga cikin farji da matse kan zakari da hannu (squeeze and pause technique/penis grip) a lokacinda mutum yake akan hanyar kawowa.