Kankana ta kasance daya daga cikin manyan kayan itatuwa masu matukar muhimmanci a jikin dan adam ta bangarori da dama, musamman idan mu kayi duba da irin gudunmawar da take bayarwa wajen bada kariya daga kamuwa da cututtuka, har zuwa ga alfanunta wajen gyaran fata da kuma, uwa-uba kore yunwa.
Sakamakon mutane da dama sun santa, kuma ana yawan amfani da ita, amma idan aka tambayi wasu amfanin ta, babu lallai su fada maka amfaninta ga lafiya guda uku, wannan dalili ne yasa muka yanke shawarar kawo muku amfanin kankana a jikin dan adam.
Ga wasu daga cikin amfanonin ‘ya’yan kankana a jikin dan adam:
1. ‘Ya’yan kankana suna water da jikin dan adam da sinadaran magnesium wanda ke taimakawa zuciya wurin harba jinni da kuma magance ciwon diabetis.
2 .‘Ya’yan kankana suna da sinadarin lycopene wanda keda kyau ga fuskar dan adam da kuma kara lafiyar namiji.
3. ‘Ya’yan kankana suna samar da sinadarin multivitamin B, wanda yana karawa jiki lafiyar jinin dan adam.
4. ‘Ya’yan kankana ana amfani dasu wurin magance ciwon diabetes, idan aka tafasa ruwa ‘ya’yan kankana 1litre na tsawon mintina 45, sai a ringa shan ruwan kamar shayi.
5. ‘Ya’yan kankana suna taimakawa wurin samun karfin jiki bayan rashin lafiya sannan kuma suna kara kaifin tinani.