Juna biyu abu ne wanda ma’aurata k enema da zaran an daura aure.
A wani lokaci ana samun matsalar rashin samun juna biyu kuma wannan ya na kawo matsaloli da tashin hankali tsakanin ma’aurata.
Rashin samun ciki na iya kasancewa daga bangaren mata ko miji. Ma’ana ba duk rashin samun juna biyu ke zama laifin mace kadai ba.
Ayau zamu yi bayani gameda ABUBUWAN DA KE IYA HANA MACE DAUKAR CIKI da suka shafi mace.
1. Matsalolin al’ada ko period. Idan mace ta kasance al’adar ta bay a zuwa a lokacin da ya kamata ko kuma ta iya wata uku ko hudu bata ga al’ada ba to tana iya samun rashin daukar ciki da sauri. Wannan matsala na bukatar a tafi asibiti domin ayi mata gwaje-gwajen jinni domin duba yawan sinadaran hormones da ke a cikin ta. Wannan matsalar ana iya shawo kanta da ikon Allah.
2. Tsufa ko yawan shekaru ga ya mace. Daukar cikin farko bayan mace ta haura shekara 30 na iya zuwa da wasu matsaloli kamar zubewan ciki da haihuwar yaro mai wata nakasa. A lokacin da mace ta ke da shekaru 17 ko abin da yayi sama amma bai kai talatin ba to tafi samun ciki mai lafiya. Domin tana da cikakkar lafiyar samun juna biyu cikin sauki.
3. Endometriosis: Rashin lafiya ne wanda ke iya sa wani bangaren mahaifa yai kauri da karfi ta yanda zai hana kwan da namiji da kwan ya mace su hadu. Kuma hakan ya iya hana daukar ciki ga mace. Ana iya gano wannan matsala kuma a magance ta a asibiti
4. Kiba mai yawa ko rama mai yawa gay a mace. Idan mace ta na da kiba sosai ko kuma mace tana da rama sosai ta na iya daukar tsawon lokaci kafin ta dauki ciki. Akwai gwaje-gwajen da za a yi a asibiti kuma aba da shawarwari ko magani a asibiti
5. Rashin ni’ima ko ruwan bakin mahaifa. Idan bakin mahaifar mace ya kasance busashshe ya na iya hana kwan da namiji samunsukunin shiga mahaifa bayan saduwa. Wannan ya na iya hana mace daukar ciki
6. Infection wanda ba a magance shi ba. Akwai mata da dama masu infection amma basa shan magani akan ka’ida. A irin wannan halin infection din na iya mamaye mahaifa ko kuma ya mamaye maran mace kuma ya hana ta daukar ciki
7. Matsalolin halittar mahaifa ko toshewan mahaifa idan mace ta na da fibroid. Wannan a asibiti za a tabbatar da shi kuma a gaba magani ko kuma ayi wa mace theatre.
Allah Ya sa mu dace Ameen.