Wasu mutanen da dama suna ta’allaka kumburin gaban mace a matsayin wani nau’i na ciwon sanyin kara, wanda za’a iya yarda da hakan duba da yadda sanya fatar jikin mutum ta dauki iska, ko kuma ruwa a jikinta.

Kumburin gaban mace yana faruwa ne sakamakon wasu yanayi masu tarin yawa dake jikin dan adam, musamman jinsin mata. Bisa wannan dalili yasa zamu kawo muku hanyar da zaku bi domin magance ta cikin sauƙi.

Sau da yawa magance cuta ko jinya baya nufin warkar da ita gaba daya ne, a’a yana dai rage zafi da kuma radadin ciwon ga mutum ne kawai. Amma cikin ikon Allah, wanda shine me kaddara komai, sai a samu sauki har a rabu da jinyar ko cutar gaba daya.

Ga dukkan masu bukatar wannan hadi, sai a nemi abubuwan da zan lissafo domin neman dacewa a wurin ubangiji.

Zaki nemi kayan hadi kamar haka;

Garin Magarya
Garin Hulba
Garin Tafarnuwa
Man Shanu

Yadda zaku haɗa wannan magani;

Bayanin yadda za’a hada abu ne mai saukin gaske, kuma ba’a fiya yawan samun matsala ba wajen yinsa.

Zaki samu wadannan kayan hadin sai ki hadesu guri daya ki gauraya sai ki kwaba da man shanu ki dunga matsi da shi.
Da yardar Allah zakiga cigaba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *